in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne Usain Bolt ya shiga kungiyar wasan kwallon kafa ta Jamaica
2014-03-17 16:43:10 cri
Bisa labarin da kafar yada labarai ta kasar Jamaica mai suna "The Sunday Gleaner" ta fitar, an ce babban kocin kungiyar wasan kwallon kafar kasar Jamaica Winfried Schaefer, ya bayyana a farkon wannan wata cewa, yana fatan Usain Bolt, zai shiga kungiyarsa, inda zai shiga wasan share fagen gasar kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2018.

Kafar labaran ta ce tuni Usain Bolt ya bayyana cewa, akwai yiwuwar hakan.

Schaefer dai wanda shi dan asalin kasar Jamus ne, ya ce a farkon wannan wata da muke ciki ne ya samu labarin aniyar Usain Bolt din ta shiga fagen taka leda, kuma ana rade radin cewa zai shiga kungiyar Manchester United ne. Shi dai kasancewar sa dan kasar Jamaica, Schaefer na fatan zai shiga kungiyar kasar ta Jamaica domin taka leda. Yace akwai yuwuwar Bolt ya shiga wannan kungiya, bayan wasan Olympic na shekarar 2016, kamar yadda ya nuna sha'awar sa ga harkar kwallon kafar.

Kiran da Schaefer ya yiwa wannan gwanin tsere, da ma bayyana yuwuwar amsa wannan bukata da Bolt din ya yi, na ci gaba da janyo hankalin masu sha'awar wasannin motsa jiki.

Shi dai Bolt mai matukar kaunar wasan kwallon kafa ne, amma ba wanda zai iya sanin kwarewarsa a wannan fage na kwallon kafa, saboda babu wanda ya taba ganin sa yana taka leda. An ce, duk da haka akwai yiwuwar buga wasu wasanni, idan har ya nuna kwarewarsa.

Bugu da kari, game da batun 'yan kasuwa masu daukar nauyin kulaflikan kwallon kafa, a cewar Schaefer, idan har Bolt ya shiga kungiyarsa, akwai karin damar samun masu sha'awar kwallon kafa da za su cika filin wasa, matakin da zai zama wata babbar dama mai kyau ta samun karin riba.

Ban da haka, Schaefer ya kara da cewa, za su iya baiwa Bolt horo mai kyau, ta yadda zai zama wani fitaccen dan wasan kwallon kafa. Kowa dai ya san yana da gudu sosai, don haka za a iya bashi horon hada gudun sa da dabarun kwallon kafa, ta yadda zai zama daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a wannan duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China