Rahotanni sun bayyana cewa, birnin na Salvador, dake Arewa maso Gabashin kasar ta Brazil, zai dauki wannan mataki ne, da nufin jawo hankalin 'yan yawon shakatawa da za su halarci gasar cin kofin duniyar da a yi a kasar. Bugu da kari mahukuntan burnin na fatan bikin, zai share wata hanya ta tallata al'adun yankin ga 'yan yawon shakatawa.
A cewar wata jaridar birnin mai suna Folha de Sao Paulo, masu raye-raye zasu karade titunan birnin 15 suna rera wakokin wasu mawakan kasar 2.
Bisa al'ada dai ana gudanar da bikin kade-kade da raye rayen shekara-shekara a kasar ta Brazil ne, a watannin Fabarairu da Maris, domin murnar karatowar bikin Ista, na mabiya addinin kirista.(Saminu Alhassan)