in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar kasar Brazil ta yi Allah wadai da batun nuna bambancin launin fata
2014-03-11 15:11:11 cri

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta nuna damuwarta, don gane da abkuwar wani lamari mai nuni ga nuna wariyar launin fata, wanda har yanzu ke aukuwa a harkokin wasannin kwallon kafar kasarta, wadanda kuma ke shafar wasu 'yan wasa da jami'an kasar.

Bisa kalmomin da ta rubuta kan shafin ta na Twitter, shugaba Rousseff ta nuna goyon baya ga Arouca, wani dan wasan tsakiya da aka wulakanta, saboda launin fatansa, yayin da yake madadin Santos a karawar kulaf din kasar da Mogi Mirim, yayin wani wasa daya gudana a jihar Sao Paulo ran Alhamis 6 ga wata.

A cewar shugaba Rousseff, ba za a yarda da wannan dabi'a ta bayyana ra'ayin nuna bambancin launin fata a kasarta ba, duba da yadda kasar ke cike da al'umma bakar fata masu dinbin yawa.

Lamarin dai yazo kwana guda, bayan da wasu masu sha'awar kwallon kafa suka yi wa alkalin wasa Marcio Chagas ihu, lokacin da yake hura wasan da Edportivo da Veranopolis suka buga.

Kafin haka kuma, a watan Fabrairun bana ma, magoya bayan kulafi din Real Garcilaso, su yiwa dan wasan tsakiyar kasar ta Brazil Tinga ihu, a gasar Copa Libertadores da aka buga a kasar Peru.

A nata bangaren, Shugaba Rousseff ta yi alkawarin mai da yaki da nuna wariyar launin fata wani babban jigon gasar cin kofin duniya na bana. Tana mai cewa kasar ta, da hadin gwiwar MDD da hukumar FIFA, sun amince da tabbatar da wannan buri, na yakar duk wani yanayi dake nuni ga wariyar launin fata.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China