in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NFA ta gabatarwa 'yan wasan Najeriya tsarin da ya dace su bi
2014-03-11 15:56:47 cri
Hukumar gudanarwar kwallon kafa ta Najeriya NFA, ta kaddamar, tare da mika wani kundi, mai kunshe da tsare-tsare, da ka'idoji da ya zama wajibi 'yan wasa, da jami'ansu su kiyaye, yayin da suke wakiltar kasar a manyan gasanni, gabanin fara gasar cin kofin duniya dake tafe nan da 'yan watanni a kasar Brazil.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya samu kwafin ta, ta rawaito shugaban hukumar ta NFA Aminu Maigari, na cewa kundin na dauke da cikakkun bayanai, dake fashin bakin abubuwan da ya kamata 'yan wasan, da kuma jami'an su lura da su. Kundin bayanan da a cewar Maigari an tsara shi ne da kyakkyawar niyya.

Sanarwar ta kara da cewa, kiyaye ka'idojin da ke zayyane cikin kundin mai shafuka 18, zai tabbatar da nasarar 'yan wasan musamman yayin manyan wasanni da tawagar ta Najeriya za ta buga. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China