Sakamakon wasannin sada zumincin da aka buga ran 5 ga watan nan ya nuna cewa, kasar Aljeriya ta kai bantanta, bayan da ta sanyawa kulaf din kasar Slovenia kwallaye 2 a zare, ta hannun 'yan wasanta El-Hilal Soudani da kuma Saphir Taidert, aka kuma tashi Slovenian na nema.
Aljeriya dai za ta kara ne da kasashen Belgium, da Koriya ta Kudu, da kasar Rasha a rukunin H (8), na gasar cin kofin na duniya dake tafe a watan Yunin dake tafe.
Su kuwa kasashen Kwadebuwa da Najeriya kunnen doki suka yi a nasu wasannin. A wasan da Kwadebuwa ta buga da kasar Belgium, a birnin Brussels an tashi ne 2-2, bayan da Didier Drogba, da Max Gradel suka tefawa kasar su wadannan kwallaye a zaren Belgium.
Yayin wasan Najeriya da Mexico kuwa an tashi ne kowa na nema. Wasan wanda aka buga a filin Georgia Dome, na birnin Atlanta ya samu halartar 'yan kallo sama da dubu 68. Mexico dai ta samu damammaki da dama na jefa kwallo a zare amma hakan ta ci tura. Har wa yau mai tsaron gidan kungiyar Najeriya Vincent Enyeama ya kade wasu hare hare masu hadari da aka kaiwa kungiyar sa.
A gasar cin kofin Duniya dai Najeriya za ta kara ne da kasashen Argentina, da Bosniya Herzegovina, da kuma Iran.
Ragowar kasashen Afirka da zasu halarci gasar cin kofin na duniya wato Kamaru da Ghana kuwa, faduwa suka yi ba nauyi. Inda a wasan sada zumunci tsakanin Kamaru da Portugal, 'yan wasan Portugal din ne suka lallasa Kamaru da ci 5 da 1. Cristiano Ronaldo ne dai ya fara jefa kwallo a zaren Kamaru tun kafin wasa ya yi nisa, sai kuma kwallon Vincent Aboubakar wanda ya farkewa Kamarun daf da tafiya hutun rabin lokaci. Amma jin kadan da dawowa daga hutun rabin loakacin ne labari ya sauya, inda 'yan wasan Portugal din suka karawa Kamaru kwallaye 4 a zare.
Kamaru dai zata fafata ne da kasashen Brazil, da Croatia, da kuma Mexico a rukuni na Farko (A), yayin gasar cin kofin duniyar da Brazil zata dauki nauyin bakuncin sa.
Haka dai labarin yake ga kasar Ghana, inda ita ma Montenegro ta ci ta kwallo daya mai ban haushi, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda Dejan Damjanovic ya buga, yayin wasan sada zumunci da suka buga a birnin Podgorica. Idan Allah ya kaimu watan Mayun dake tafe, Ghana za ta kwashi 'yan kallo ne da kasashen Jamus, da Portugal, da kuma kasar Amurka, a rukunin na 7 (G) na gasar cin kofin duniyar dake tafe.(Saminu Alhassan)