Da ma dai an yi shirin bude filin wasan ne a birnin Cuiaba dake yammacin kasar Brazil a ranar 22 ga watan nan na Maris, sai dai masu aikin sa sun kasa gama aikin ginin filin zuwa karshen watan Disambar bara, wa'adin da hukumar kwallon kafan duniya FIFA ta sanya.
An ce dalilin da ya sa aka sake dakatar da bude filin wasan a wannan karo shi ne, domin wani kamfanin kasar Brazil mai kula da aikin gina filin ya kasa sanya kujeru 42,000, da ake bukatar su a filin cikin lokacin da aka kayyade.
Cikin filin wasan Arena Pantanal ne kungiyoyin kasashen Chile da Australia, za su buga wasan farko na gasar cin kofin duniya na wannan karo a ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa.
Sauran wasannin gasar da aka yi shirin gudanarwa a filin wasan sun hada da, wasannin da za a yi tsakanin Rasha da Koriya ta Kudu, da na Nijeriya da Bosnia, da kuma tsakanin Japan da Colombia.(Bello Wang)