Idan an yi la'akari da yadda kulaf din Juventus ya lashe Fiorentina da ci 1 da nema, wanda ya sanya gibin dake tsakanin Juventus da Roma habaka zuwa maki 14, hakika hakan ya wuce karfin Roma ta shawo kan sa ta ko wane irin hali.
Garcia ya ce duk da cewa ba a kammala wasannin wannan kakar wasa ba tukuna, amma a hakika yanzu ma ana iya tabbatar da sakamakon ta. A cewarsa babban gibin da ke tsakanin Juventus da Roma yanzu haka, ya talastawa kungiyarsa, kokarin samun nasara a wasa mai zuwa, wanda zai gudana a gidan kulob din. Ya ce yana fata wasu 'yan wasansa za su farfado daga raunukan da suka ji zuwa lokacin.
A nasa bangaren, babban kocin kulob din Juventus, Antonio Conte, ya ce Juventus din ya kaiga cimma nasarar kashi 50% na zakaran kasar Italiya a bana. A cewarsa, sauran wasanni 11 a kammala gasar Serie A, amma tuni kulob din ya riga ya ci rabin nasarar da yake bukata, kuma yana kan hanyar samun babbar nasara a karshe, sai dai ya kara da cewa, sauran kuloblika ba za su nade hannu su bari Juventus ya zama zakara ba tare da sun gwada nasu kokari ba.(Bello Wang)