in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane 200 ne suka rasa rayukansu a dauki ba dadin da auku a birnin Maiduguri
2014-03-15 20:43:27 cri
Rahotanni daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, dake Arewa maso Gabashin tarayyar Najeriya, na cewa mutane a kalla 212 ne suka rasa rayukansu, sakamakon dauki ba dadin da sojoji suka yi, da mayakan kungiyar Boko Haram.

Dauki ba dadin da aka kwashe sa'o'i kimanin 6 ana yi a jiya Jumma'a, a cewar kafafan watsa labarun kasar sun rutsa da sojoji 5, baya ga ragowar mutane sama da 200, da ake kyautata zaton magoya bayan kungiyar ta Boko Haram ne.

Rahotanni sun ce tun da fari, maharan sanye da kayan sarki ne suka kaddamar da hari kan barikin sojin dake birnin na Maidguri a kokarinsu na kwato 'yan uwansu dake tsare a barikin, inda kuma nan take soji suka bude musu wuta.

Shaidun gani da ido sun ce samari masu aikin sa kai da ake wa lakabi da "Civilian JTF", sun damke da dama daga maharan dake kokarin tserewa yayin musayar wutar, suka kuma mika su ga sojoji.

Jihar Borno dai ita ce babbar maboyar 'ya'yan wannan kungiya, wadda kuma kawo yanzu, ita da jihohin Yobe da Adamawa ke karkashin dokar ta baci, wadda gwamnatin tarayyar kasar ta kafa musu, sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro da suke fuskanta. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China