0308bagwai
|
A farkon makon jiya ne a kulla wannan yarjejeniya yayin wani biki na ban kwana da aka shiryawa rukunin farko na dalubai 50 da suka tashi zuwa kasar ta Masar.
Daluban dai zasu kwashe shekaru uku ne suna karatun degree a fannin jinya da ungowar zoma a wanann jami`a ta Al-Mansoura dake kasar ta Masar.
A cikin jawabin sa Gwamnan Kano Rabi`u Musa kwankwaso ya ce gwamnati ta kashe naira miliyan 303 wajen daukar nauyin wadannan dalubai, kuma ana sa ran idan sun kammala karatun nasu zasu dawo gida domin koyarwa a sabbin makarantun kiwon lafiya uku da gwamnatin ta kirkiro a kananan hukumomin Bebeji, Madobi,da Gabasawa.
Haka kuma gwamnatin jihar Kano ta dauki wasu malamai `yan kasar Masar su goma aiki daga jami`ar ta Al- Mansoura domin su fara bayar da horo a wadannan sabbin kwalejojin kiwon lafiya uku kafin dawowar daluban.
Dr. Rabi`u Musa Kwankwaso ya cigaba da cewa gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin magance matsalar karancin ma`aikatan jinya a asibitoci mallakar gwmanatin jihar.
Yace irin wannan hali da bangaren lafiya ke ciki ya sanya gwmanati kulla wannan yarjejeniya da Jami`ar Al-Mansoura, inda yace a karkashin wannan yarjejeniya jami`ar zata rinka tura malamai daga kasar ta Masar a duk watanni uku domin su rinka gudanar da ayyuka a asibitoci daban daban dake jihar, kari kan malaman da zasu rinka koyarwa a wadancan sabbin kwalejoji.
Dr. Rabi`u Musa kwankwaso ya kara tabbatar da cewa a shekara karatu mai kamawa, gwamnatin Kano ta na da shirin sake daukar nauyin `yan asalin jihar wadanda suka kammala karatun sakandire su dari 5 domin yin karatu a bangaren kiwon lafiya a jami'o'i daban daban na duniya.
A sabo da haka ya yi kira ga daluban da suka tashi zuwa kasar Masar dasu kasance jakadun jihar nagari, tare da kaucewa shiga kungiyoyin tayar da hargitsi .
A Lokacin da take nata jawabin , wakiliyar hukumar UNICEF ta majalissar dinkin duniya Madam Melissa Carkum cewa tayi sanya jari wajen horas da malaman jinya, tamkar sanya jari ne wajen kyautata rayuwar mata da kananan yara, kuma matakin da gwmanatin Kano ta dauka ya zo dai dai da manufar shirin hukumar ta UNICEF .
Daga bisani ta bayar da tabbacin cewa hukumar ta UNICEF zata cigaba da bayar da hadin kan ta da goyon bayan ga gwamnatin jihar Kano wajen yaki da ciwon polio.
Daga karshe a cikin jawabin sa , shugaban Jami`ar Al-Mansoura Farfessa Ahmed Abdul Khalid cewa yayi jami`ar tana daya daga cikin manyan jami`oi uku dake kasar ta Masar da sukayi fice wajen samar da ilimi mai nagarta, kuma yayi alkawarin cewa jami`ar a shirye ta ke ta bayar da gudumowa wajen kyautata sha`anin aikin lafiya a jihar Kano.
Tsoffin gwamnonin Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki dana Cross Rivers Donald Duke na daga cikin manyan baki da suka halarcin bikin, inda suka yaba bisa yadda a dan kankanen lokacin gwmanan Kano Rabi`u Musa Kwankwaso ya sauya fasalin jihar a fagen kiwon lafiya, walwala da tattalin arziki.(Garba Abdullahi Bagwai)