Hoton da aka buga a shafin sada zumunta na zamani dai ya nuna yadda 'yan sandan kasar ta Afrika ta kudun suka yi ma wani dan Nigeriya dukan fitar arziki wanda ya jawo ka-ce-na-ce game da yadda kasar ke yi ma baki musamman akan shaidar da aka yi mata na kyamar bakin.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Nigeriya Ogbole Ode a cikin sanarwar da ya fitar kuma kamfanin Xinhua ta samo kwafi a Abuja, ya ce ofishin jakadancin kasar dake Pretoria tana bincike a kan cin zarafin da aka kai ma mutumin mai suna Clement Emekeneh.
Mr Ode ya ce ofishin ta riga ta aika da wasikar nuna rashin jin dadinta da babbar murya ga sashin kula da harkokin kasashen waje na kasar Afrika ta kudun tare da bukatar a gurfanar da wadanda suka aikata hakan a gaban kuliya.
A cewar shi yanzu haka an riga an tabbatar da cewar 'yan sanda kasar su biyu da suka yi wannan danyen aiki na yi ma Clement dukan fitar arziki an kama su tare da dakatar da su kuma za su fuskanci shari'a. A don haka in ji shi ofishin jakadancin Nigeriya a Pretoriyan za ta ci gaba da sa ido a kan batun har sai ta ga an bi ma dan Nigeriyan nan hakkinsa.
Kakakin ma'aikatan harkokin wajen na Nigeriya daga nan sai ya tabbatar ma 'yan Nigeriya cewa gwamnati ba za ta taba amincewa a ci ma 'yan kasar ta mutunci ba a ko ina suke.