0302murtala
|
Rundunar 'yan sanda a Najeriya sun tabbatar da cewa harin Bam din da aka kai har sau biyu a wani waje da ake ta hada hadar yau da kullum a garin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin kasar ya hallaka mutane 35.
A bayanin da kwamishinan 'yan sandan jihar Lawan Tanko yayi ma Xinhua ta wayar tarho yace wani bam da ake zargin 'yan kungiyar boko haram ne suka dana shi a kusa da wassu shaguna ya tashi kuma a cikin mintoci biyu wani ya kuma tashi abin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama don haka 'yan sanda na cigaba da bincike sannan 'yan bada agajin nata iyakacin kokarin su.
Wani ganau Mohammed Buba yace bam din ya tashi ne da misalign karfe 6 na yammaci lokacin da galibin mazauna wajen ke kokarin zuwa sallar Mangariba. Yana mai bayanin cewa bam din an nade su cikin tsanaki a motar sai da itace da ake zaton anyi dakon shi ne daga dajin Sambisa dake karamar hukumar Damboa.
Ya zuwa lokacin da labarin ya iso mana babu wani mutum ko kungiya da suka dauki nauyin kai harin,duk da dai cewa Maiduguri ya zama cibiyar kungiyar ta boko haram,kungiyar da take barazana wajen kai hare hare a Najeriya kuma ta zama karfen kafa ga jami'an tsaron kasar tun shekara ta 2009.
Game da lamarin wakilinmu dake Najeriya Murtala ya yi hira da Malam Babagana Hamidu wani mazaunin Maiduguri wanda gidansa ya yi kusa da wajen abkuwar lamarin, bari mu saurari bayanin da Malam Babagana ya yi dangane da batun.