Fedotov wanda ya bayyana hakan a jiya Jumma'a ya ce batun aiwatar da yarjejeniyoyin da suka shafi yaki da yaduwar kwayoyi masu sanya barci, da rage samarwa da bukatar amfani da magunguna barkatai, da ma sauran batutuwa masu alaka da hakan, na cikin manyan kalubalen dake gaban hukumar.
Mr. Fedotov wanda ya bayyana hakan yayin taron kwamiti mai lura da harkokin da suka shafi yaduwar magungunan masu sa barci na MDD, ya kara da cewa, an samu sakamako mai kyau game da aikin hana yaduwar magungunan barkatai, sai dai ofishin na UNODC na ganin cewa, ana fuskantar kalubaloli da dama a fannonin aiwatar da yarjejeniyoyin hana yaduwar magungunan sa barci da sassa masu alaka da hakan.
Ya ce kamata ya yi kasashen da batun ya shafa su mai da hankali kwarai, wajen tattaunawa kan wannan lamari, domin shawo kan matsalar yadda ya kamata. (Maryam)