A cikin sakon ta faifan video, Mr Ban ya fara gabatar da kansa, sannan ya mika sakon murnar sabuwar shekarar gargajiyar cikin harshen Sinanci, inda ya ce yana mika fatanshi na alheri ga daukacin al'ummar Sinawa da iyalansu a lokacin da ake bikin shekarar doki. Kuma yana masu fatan kasancewa cikin koshin lafiya, farin ciki da nasara a cikin shekarar da za ta kama.
Babban magatakardar ya kuma mika godiyar ga al'ummar Sinawa, yana mai cewa abin alfahari ne ga Majalissar da take aiki tare da su don cimma burin zaman lafiya, ci gaba da samar da 'yancin dan Adam. Yana godiya dangane da sadaukarwarsu da gudummuwa.
Bikin bazara shi ne muhimmin lokacin hutu ga al'ummar Sinawa, inda 'yan uwa suke haduwa guri guda a ko'ina don sada zumunci. (Fatimah)