A cewar kakakin MDD Martin Nesirky, za a bukaci taimakon kudi daga kasashen duniya, da yawansu zai kai dalar Amurka miliyan dubu biyu, domin baiwa al'ummun yankin na Sahel tallafin kandagarki daga yunwa, da karancin tsaro kamar yadda shugabar sashen kula da ayyukan jin kai na majalissar Valerie Amos ta bayyana yayin kaddamar da sabon shirin ranar Litinin a birnin Rome na kasar Italiya.
A nasa tsokaci babban daraktan hukumar aikin noma ta MDD Jose Graziano da Silva, cewa ya yi cikin manufofin sabon shirin akwai samar da nagartattun kayan noma da za su inganta yabanyar da manoman yankin za su shuka a kakar bana.
Sabon shirin na wannan karo dai ya kunshi tanaji na musamman ga kasashen Chadi, da Burkina Faso, da Kamaru da Gambia. Sauran kasashen sun hada da Mali, da Mauritaniya, da Nijar, da Senegal da kuma Najeria. (Saminu Alhassan)