Mr. Ban ya yi wannan kira ne yayin da ya ke gabatar da jawabinsa na farko a wannan shekara ga babban taron MDD mai mambobi 193 (UNGA), inda ya tabo kadan daga cikin kalubalen da majalisar za ta fuskanta a shekara ta 2014, da jaddada ci gaban tashin hankali a kasashen Syria, Sudan ta kudu, Afirka ta tsakiya, Jamhuriyar demokiradiyar Congo da dai sauransu.
Ban Ki-mmon ya ce, Allah ya albarkaci wadannan kasashe da ke fama da tashin hankali albakarbatu, 'yan kasa masu amfani, tarihi da kuma damar samun zaman lafiya da makoma mai haske a kowane lokaci, don haka ya ce wajibi ne shugabanni su dauki matakan da suka dace, ta yadda wadannan kasashe za su amfana da wadannan albarkatu.
Bugu da kari, babban sakataren na MDD, ya bukaci da a kara kokari game da wa'adin da aka tsayar na kawar da talauci a shekara 2015 tare da amincewa kan taswirar da za ta zayyana manufiofin da za a cimma bayan shekarar ta 2015. (Ibrahim Yaya)