in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe 'yan Boko Haram a wata musayar wuta
2014-03-14 20:42:52 cri

Wani labari da dumi-duminsa na cewa, dakarun Najeriya sun kashe 'yan kungiyar Boko Haram da dama bayan da suka kai hari a barikin soja da ke garin Maiduguri, a kokarin da suke yi na kubutar da mambobinsu da ake tsare da su.

Kakakin hedkwatar sojojin Najeriya Chris Olukolade ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, inda ya ce, sojojin sun murkushe wani harin da 'yan kungiyar suka shirya kaiwa a garin na Maiduguri.

Jami'in ya ce, sojojin sun kuma yi nasarar kwace makaman maharan tare da kama da dama daga cikinsu. Ya kuma bayyana cewa, sojoji hudu sun ji rauni a gumurzun, kuma yanzu haka a na yi musu magani

Ya ce, yanzu haka sojojin suna ci gaba da farautar maharan ta sama da ta kasa, a kokarin da ake na kawo karshen hare-haren da suke kaiwa a yankin.

Tun a shekarar 2009 ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kasance babbar barazana ga kasar ta Najeriya, inda suka halaka daruruwan mutane cikin watanni 3 da suka gabata ta hanyar kai hare-hare kan kauyuka da dama da ke sassa daban-daban na jihohi 3 da ke shiyar.

Wakilinmu dake Abuja Murtala ya zanta da Malam Babagana Hamidu wani mazaunin garin na Maiduguri dangane da halin da ake ciki, ga kuma abin da ya ke shaida masa. (Ibrahim Yaya)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China