in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari a garin Maiduguri da ke Najeriya
2014-03-14 20:12:58 cri
Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno na cewa, an shafe sa'o'i biyu ana jin karar bindigogi da fashewar abubuwa.

Wasu mazauna garin sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka afkawa birnin, inda ake fargabar mutane da dama sun jikkata.

Sai dai wani mazaunin garin na Maiduguri mai suna Aliyu Gambo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, mai yi wa harin na yau, mayar da martani ne kan hare-haren da sojoji suka kaiwa kungiyar a dajin Sambisa da sauran maboyarsu.

Ko da yake babu wasu bayanai game da yawan wadanda suka mutu ko suka jikkata, amma hukumomin sun shaida wa manema labarai cewa, sojoji sun shawo kan lamarin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China