Jami'an tsaro a tarayyar Najeriya, sun ce, dakarun sojin kasar sun harbe mayakan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram su 20, yayin wani simame da aka kaddamar a sassan jihar Borno.
Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar tsaron kasar Chris Olukolade ya fitar jiya a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, ta ce, dakarun rundunar sojin sun kuma dakile yunkurin 'ya'yan kungiyar, na kaddamar da wasu hare-hare a unguwannin Ajiri da Mafa, da kuma garin Dikwa da karkarar birnin Maiduguri, helkwatar jihar ta Borno.
Sanarwar ta bayyana cewa, baya ga makamai, da ababen fashewa da aka gano a maboyar 'ya'yan kungiyar, an kuma lalata sansanoninsu dake wurare daban daban, a jihar ta Borno da kuma jihar Adamawa.
Mahukunta a Najeriyar dai sun sha nanata aniyar kakkabe ayyukan kungiya ta Boko Haram daga kasar, musamman ma jahohin arewa maso gabashin kasar, jahohin da suka fi fama da hare-haren magoya bayan kungiyar.
A hannu guda kuma Boko Haram din na dada tsananta kai hare-hare, inda ko da a makon da ya gabata, sai da mayakanta suka hallaka wasu 'yara 'yan makaranta su 29 a jihar Yobe. Kari kan daruruwan fararen hula da suka rasa rayukansu, sakamakon hare-haren kungiyar tun daga shekarar 2009 da ta gabata. (Saminu)