Rundunar sojin tarayyar Najeriiya, ta ce, ta cafke wasu mayakan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, a wani wuri dake daf da iyakar kasar da tafkin Chadi.
Daraktan watsa labaran rundunar Chris Olukolade ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Olukolade ya ce, cikin wadanda aka damke, akwai wadanda suka samu kubuta da raunuka, daga hare-haren da jami'an tsaro suka kai sansanonin su a baya bayan nan. Baya ga wasu da dama da suka fada hannun sojojin a garuruwan Dikwa, da Cross Kauwa, da Kukawa da kuma Alargarmo.
Haka zalika sanarwar ta ce, tuni wadanda aka kame suka fara ba da muhimman bayanai game da halin da kungiyar take ciki, da ma yadda karancin abinci, da hare-haren da ake kai musu ya tilasta su yin watsi da sansanoninsu.
Sanarwar ta kuma ruwaito Olukolade na cewa, dakarun sojin kasar na ci gaba da kara azamar kaddamar da hare-hare, kan sansanonin mayakan kungiyar ta Boko Haram, a daukacin jahohin nan uku dake karkashin dokar ta baci. (Saminu)