Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa, yanzu haka ana fuskantar matsalar daukewar layukan wayoyin sadarwar, sakamakon kokarin da dakarun sojin kasar ke ci gaba da yi, na fatattakar mayakan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.
Kakakin runduna ta 7 ta sojin kasar Mohammed Dole ne, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua hakan, yana mai cewa, ya zama wajibi daukacin al'ummar wannan yanki su yi hakuri da halin da ake ciki, domin cimma moriyar da aka sanya gaba.
Dole ya kara da cewa, sojoji na daukar karin matakan dakile dukkanin ayyukan maharan kungiyar ta Boko Haram, wadda ke kokarin daidaita rayuwar fararen hula a yankin.
Wasu mazauna jihar Borno sun tabbatar da daukewar layukan sadarwar a ranar Laraba, yayin da sojoji ke ci gaba da bincike a dajin Sambisa, da ma sauran wuraren da ake zaton mayakan kungiyar na samun mafaka.
A bara ma dai rundunar sojin kasar ta katse layukan sadarwa a jihohin Borno, da Adamawa, da Yobe har kusan watannin 6.
Gwamnatin tarayyar Najeriyar ta sanyawa wadannan jahohi dokar ta baci ne dai tun cikin watan Mayun 2013. sakamakon tsanantar hare-haren kungiyar Boko Haram a jahohin. (Saminu)