in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar soji a Najeriya na daukar sabbin matakan dakile ayyukan 'yan ta'adda
2014-02-28 09:52:42 cri

Helkwatar rundunar soji a tarayyar Najeriya ta ce, dakarunta na daukar sabbin matakan dakile ayyukan 'yan ta'adda a jahohin kasar uku dake karkashin dokar ta baci.

Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Janar Chris Olukolade ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Alhamis a birnin Abuja.

Olukolade, wanda ya yi karin haske kan halin da jahohin Adamawa, da Borno da jihar Yobe ke ciki, ya ce, sabbin matakan da ake dauka yanzu haka, za su dada dakile yunkurin da mayakan kungiyar nan ta Boko Haram ke yi, na kai sabbin hare-hare, ko ficewa daga Najeriyar zuwa makwaftan kasashe.

Ya ce, harin da mayakan kungiyar suka kai a Michika ta jihar Adamawa a baya bayan nan ma, wani yunkuri ne na kwasar ganima, a shirin su na arcewa zuwa kasar Kamaru ta kan iyakar Najeriya dake wannan sashe. Yayin dauki ba dadin da suka yi da sojojin Najeriya a Michikan kuwa, a cewarsa, an harbe mayakan 6, aka kuma kame wasu 2, tare da lalata motocin su 9. Sai kuma soja 1 da fararen hula 3 da su ma suka rasa rayukansu.

Don haka daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriyar, ya bukaci jama'ar wadannan yankuna na arewa maso gabashin Najeriya, da su sanya ido tare da ba da rahoton da ya shafi zirga-zirgar 'yan kungiyar ta Boko Haram da suka gani a yankunansu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China