Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Laraban nan ya yi suka da kakkausar murya game da kisan dalibai da dama ranar Talatan da ta gabata a wata makarantar gaba da firamare ta gwamnatin tarayya dake jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar Najeriya, yankin da ya fi fama da ayyukan ta'addancin kungiyar nan masu tsatsauran ra'ayin addini Boko Haram.
A cikin wata sanarwa da kakakin shi ya fitar, an ce, Mr. Ban ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu, yana mai fatan cewa, za'a kama masu hannu a cikin wannan ta'assa tare da gurfanar da su gaban kuliya.
A kalla dalibai 29 ne aka ba da rahoton kashe su a cikin wani harin da 'yan bindigan da ba a san su waye ba suka aikata shi a kwalejin gwamnatin tarayya dake Buni Yadi, daya daga cikin garuruwan dake jihar ta Yobe da ke fuskantar hare-hare na kungiyar.
Babban magatakardar na MDD ya nuna matukar damuwar shi game da karuwan tashin hankali da hare-hare na rashin imani a makarantu dake wannan yankin, inda ya jaddada cewa, babu wani dalilin da ya cancanci tashin hankali. (Fatimah)