in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar soji a jihar Yoben Najeriya ta yi wa dokar hana zirga-zirga jama'a gyaran fuska
2014-03-01 20:24:26 cri
Rundunar sojin Najeriya dake aiwatar da dokar ta baci a jihar Yobe, dake Arewa maso Gabashin kasar ta sauya wa'adin dokar hana zirga-zirgar jama'a a kananan hukumomin Michika da Madagali.

Dokar wadda a da take fara aiki daga karfe 11 na dare zuwa karfe 5 na safiya, a yanzu za ta rika fara aiki ne tun daga karfe 7 na dare zuwa karfe 5 na safiyar kowace rana.

A cewar jami'in hulda da jama'a na rundunar Kaftin Jafaru Nuhu, wannan sauyi ya biyo bayan karuwar hare haren da ake kaiwa fararen hula a yankunan.

Kaftin Nuhu ya ce wannan sauyi zai ci gaba da aiki a dukkanin garuruwa, da kauyukan dake wadannan kananan hukumomi, har ya zuwa wani lokaci a nan gaba.

Daga nan sai ya bukaci daukacin al'umma, da su baiwa jami'an tsaro cikakken goyon baya wajen kai rahoton duk wani, ko wasu da bu amince da take-takensu ba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China