0302bagwai
|
Babbar sakatariyar hukumar Farfesa Fatimah Umar ce ta tabbatar da hakan lokacin da take zantawa da manema labarai a birnin Kano.
Farfesa Fatimah Umar tace shirin yaki da jahilcin da hukumar ta fara tun a 2012, an kirkiro shi ne domin warware matsalar jahilci a tsakanin al`ummah, inda ta ce a bara hukumar ta bayar da horo ga malamai 16,148 wadanda zasu ilimintar da magidantan.
Ta cigaba da cewa ko a cikin wannan shekara ta 2014 hukumar ta sake horas da wasu malaman 16,148, ha` ila yau an horas da jami`ai masu sanya idanu kan shirin su 444.
Farfesa Fatimah Umar ta tabbatar da cewa hukumar UNESCO ta Majalissar dinkin duniya ta zabi jihar Kano a matsayin cibiyar farfado da tsarin ilimin manya a arewacin Najeriya , bayan nazartar irin gudumowar da gwamnatin jihar Kano ke bayarwa wajen gangamin yaki da jahilci a tsakanin al`ummah.
Daga bisani babbar sakatariyar hukumar lura da ilimin manya ta jihar Kano, farfesa Fatimah Umar tace gwmnatin jihar Kano ta samar da cibiyoyin koyar da ilimin manya 8,074 a daukacin kananan hukumomi 44 dake jihar a 2013. Haka ma a cikin wannan shekarar gwamnati ta sake samar da makamancin wannan adadi domin tabbatar da ganin an yaki jahilci.
Matsalar rashin iya rubutu da karatu na daya daga cikin matsalolin dake haifar da rashin cigaban rayuwar akasarin al`umma a jihar Kano.
Bincike ya tabbatar da cewa irin wannan matsala ta fi kamari a yankunan karkara wadanda suke daukar kaso daya bisa uku na adadin yawan jama`ar jihar(Garba Abdullahi Bagwai)