Kamfanin dillancin labarai na ANI na samun labarai masu tushe kan ayyukan kungiyoyin ta'adanci dake arewacin kasar Mali.
Karamin jakada na kasar Aljeriya an sace shi tare da wasu jami'an diplomasiyya na kasar Aljeriya tun yau da kusan watanni biyar a Gao a lokacin da mayakan kungiyoyin kishin islama suka mamaye birinin.
Da farko kungiyar Mujao ta bada wa'adin kwanaki biyar ga hukumomin kasar Aljeriya domin su saki mambobin kungiyar AQMI, musammun ma mai kula da harkokin shari'a da aka kama su a makon da ya gabata.
Hakazalika gungun yayi barazanar kashe jami'an diplomasiyyar hudu da yake tsare da su idan har kasarsu bata bada kai bori ya hau ba.
Baya ga wannan gungun Mujao ya bada hoton bidiyo inda ake nuna jami'in dake kula da harkokin soja na karamin ofishin jakadancin kasar Aljeriya dake Gao na kiran al'ummar kasar Aljeriya data sanya baki domin a ceto rayukansu. (Maman Ada)