Mr. Li ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labaru da ya yi a yau Alhamis, jim kadan da rufe taro karo na biyu, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12.
Firaministan kasar ta Sin ya kara da cewa, Sin kasa ce dake martaba doka da oda, don haka dukkanin wanda ya karya doka, zai fuskanci hukunci komai kuwa matsayin sa a gwamnatance. Li ya jaddada cewa dukkanin al'ummar Sinawa matsayin su guda a gaban shari'a. (Saminu)