in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ta tsara shirin ayyukanta na shekarar 2014, a kokarin zurfafa gyare-gyaren da take yi
2014-03-05 15:48:23 cri

Yau Laraba 5 ga wata da safe ne, a nan Beijing, aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadda ita ce hukumar koli ta kasar. A yayin bikin bude taron, Li Keqiang, firaministan kasar ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati a madadin sabuwar gwamnati, inda ya jaddada muhimmancin yin gyare-gyare a gida a gaba da kome.

"Za a mai da hankali kan yin kwaskwarima ga tsarin harkokin tattalin arziki ne, duk da wahalhalun da ake fuskanta, a kokarin zurfafa gyare-gyaren da ake yi a fannoni daban daban."

A matsayinsa na firaministan kasar ta Sin,wannan shi ne karo na farko da Li Keqiang ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnatin, inda ya waiwayi ayyukan da gwamnatin Sin ta yi a shekarar bara, ciki har da gaggauta sauya rawar da gwamnati ke takawa, kyautata tsarin harkokin tattalin arziki, kara azama ga shirin bude kofar Sin ga kasashen waje, tabbatar da kyautatuwar zaman rayuwar jama'a da dai sauransu.

Dangane da manufar da kasar Sin za ta cimma a shekarar 2014 a fannin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, wadda ke jawo hankalin jama'a, rahoton ya bayyana cewa, yawan karuwar jimillar kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar Sin wato GDP zai kai ga kashi 7.5 cikin dari, tare da kokarin kara kudin shigar jama'a da bunkasa tattalin arzikin kasa a lokaci guda.

To, yaya za a cimma wannan manufar da gwamnatin ta sauya a gabanta na raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin? A cikin rahoton, an ba da amsar wadannan tambayoyi, wato za a zurfafa gyare-gyaren da ake yi a fannoni daban daban. Game da hakan, Li Keqiang ya ce, "Yin gyare-gyare a gida shi ne aiki mafi muhimmanci da gwamnatin Sin ta sanya a gabanta. Ba za a iya raya kasa ba, sai an aiwatar da shirin zurfafa gyare-gyaren da ake yi. Za mu fara da yin gyare-gyare kan fannonin da jama'ar Sin ke Allah-Allah a kai, wadanda suka hada da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, wadanda kuma sassa daban daban na kasar za su samu ra'ayi daya a kai, a kokarin barin kasuwa ta yi aikinta a fannin rarraba albarkatun kasa, kuma gwamnatin ta taka rawar sa-ido yadda ya kamata. Har wa yau za mu kara azama kan yin gyare-gyaren da za su taimaka wajen kyautata tsare-tsare, don haka dukkan al'ummar kasar za su nuna kwarewarsu,ta yadda za a tabbatar da samun adalci a kasar, kuma dukkan jama'ar kasar za su ci gajiyar gyare-gyaren da ake yi a kasar."

Kamar yadda yawancin al'ummar Sin suka sani, a cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, gyare-gyare a gida yana tare da batun bude kofar Sin ga kasashen waje ba. A cikin rahoton da Li Keqiang ya kaddamar a yau, yayin da yake jaddada muhimmancin zurfafa gyare-gyare da ake yi a kasar ta Sin, ya kuma jaddada cewa, dole ne a raya aikin bude kofar Sin ga kasashen waje zuwa sabon matsayi. Li Keqiang ya ce, "Wajibi ne a tsara sabon tsarin tattalin arziki da zummar kara bude kofar Sin ga kasashen ketare. Sakamakon takarar da ke tsakanin kasa da kasa a kasuwar duniya ya sa gwamnatin Sin ta zurfafa gyare-gyaren da take yi da kuma kyautata tsare-tsaren da take bi, da gaggauta fito da sabon fifiko na yin takara tsakanin kasa da kasa. Bayan haka kuma, gwamnatin Sin za ta tsaya tsayin daka kan yin cinikayya da zuba jari cikin sauki kuma ba tare da wani shinge ba, a kokarin samun moriyar juna da nasara tare da gamayyar kasa da kasa, ta yadda za ta iya ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje a lokaci guda kuma yadda ya kamata."

Kamar yadda gwamnatin Sin ta yi a shekarun baya, a cikin rahoton ayyukan gwamnatin na bana, gwamnatin Sin ta yi alkawarin kyautata zaman rayuwar jama'arta, inda a cewarta za ta dauki sabbin matakai a fannoni samar da guraben aikin yi, kiwon lafiya, yaki da gurbacewar muhalli, tabbatar da ingancin abinci da dai sauransu.

Nan da kwanaki 8 masu zuwa, wakilan jama'ar Sin kusan dubu 3 za su dubbaba wannan rahoto a tsanake,kana su kada kuri'arsu a bikin rufe taron. Idan sun amince da rahoton, to, gwamnatin da ke karkashin shugabancin Li Keqiang za ta gudanar da ayyuka bisa tanade-tanaden da ke cikin rahoton. Hakan zai baiwa kasar Sin damar bude wani sabon babi na zurfafa gyare-gyaren da take yi. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China