in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aiki a gun taron shekara-shekara na NPC
2014-03-05 11:05:03 cri

A ran 5 ga wata, firaministan Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aiki a gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato NPC.

Li ya ce, a shekarar bana zai sa kaimi ga samun sabon ci gaba a wasu manyan fannoni. Yin gyare-gyare ya zama aiki na farko a gaban gwamnati a bana. Za a mai da hankali sosai kan yin gyare-gyare a tsarin tattalin arziki, za a kuma kokarta wajen samun ci gaba na hakika don samar da moriya ga jama'a.

Li ya bayyana cewa, manyan fannoni da za a sanya a gaba a fannonin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a bana su ne, yawan karuwar saurin bunkasa tattalin arziki da za a samu a bana zai kai kashi 7.5 bisa dari, yawan hauhawar farashin kaya ya tsaya a kashi 3.5 bisa dari, da kuma samar da guraban ayyukan yi fiye da miliyan 10 a birane da garuruwa, kuma ana fatan jama'a da suka yi rajistar rasa ayyukan yi ya yi kasa zuwa kashi 4.6 bisa dari, kuma kudaden da Sin take cinikayya su daidaita, a kuma samun karuwar kudin shigar mazaunan Sin da bunkasuwar tattalin arziki tare.

Li ya ci gaba da cewa, a cikin shekarar da ta wuce, an tabbatar da kyautata zamantakewar jama'a a hakika, an sa kaimi ga samun adalci a zamantakewar al'umma. Ayyukan da aka gudanar sun hada da tabbatar da kyautata zaman rayuwar jama'a, da raya sha'anin ba da ilmi da yin gyare-gyare, da zurfafa gyare-gayre a fannonin asibitoci da magunguna, da sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin al'adu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China