An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na sha biyu da safiyar yau laraba 5 ga wata a nan birnin Beijing. Shugabannin kasar Sin Xi Jinping da Li Keqiang da sauran wakilai kusan dubu 3 sun halarci taron. Da farko sai da dukkan mahalartan taron suka nuna jimami ga mutanen da suka rasa rayuka a mummunan harin ta'addancin da aka kai a tashar jiragen kasa ta birnin Kunming na lardin Yunnan a ran 1 ga wata da dare.
Wannan dai ya zama taron shekara-shekara karo na farko da hukumomin ikon koli na Sin suka shirya bayan da aka yanke shawarar zurfafa yin gyare-gayre a dukkan fannoni a gun cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na 18 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Sabo da haka ne, ake sa ran mai da hankali sosai kan yadda za a aiwatar da sababbin manufofin yin gyare-gyare a rohoton farko na sabuwar gwamnati, wanda za a dudduba a gun taron.
Za a shafe kwanaki 8 da rabi ana taron. A gun taron, wakilai za su dudduba rahotannin aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da na kotun koli ta jama'a, da na babbar hukumar bin bahasin, tare da dudduba da amincewa da rahotannin shirin raya kasa da kasafin kudi.
Har wa yau a gun wannan taro, shugabannin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ciki har da shugabannin harkokin wajen, da yin gyare-gyare da raya kasa, da kasuwanci da harkokin kudi za su amsa tambayoyi daga manema labaru kan yanayin da duniya ke ciki, da manufofin diplomasiyya, da zurfafa gyare-gyare da raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kyautata zaman rayuwar jama'a da dai sauransu. A yayin taron manema labaru bayan rufewar taron a ranar 13 ga wata kuma, firaminista Li Keqiang zai zanta da manema labaru.(Danladi)