in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta jaddada damuwarta game da tserewar fararen hula daga Sudan ta Kudu da CAR
2014-03-05 10:03:58 cri

Hukumar lura da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta sake bayyana damuwarta, game da adadin fararen hula dake tserewa daga kasashen Afirka ta Tsakiya CAR da kuma Sudan ta Kudu.

Kakakin MDD Martin Nesirky ne ya bayyana hakan, yayin taron manema labaru na rana rana da ya gudana a ranar Talata, inda ya ce, dubban al'ummun kasashen biyu na tsallakawa kasashen Chadi, da Kamaru, da kuma Habasha.

Nesirky ya ce, tuni hukumar ta UNHCR ta yi kira ga kasashen duniya, da su samar da tallafin gaggawa domin baiwa 'yan gudun hijirar tallafi. A cewarsa, halin da 'yan gudun hijirar ke ciki yanzu haka, shi ne irin sa mafi muni da nahiyar Afirka ta fuskanta a baya bayan nan, wanda tuni ya tilasta kimanin mutane miliyan 1.8 kauracewa gidajensu.

Tuni dai hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta mika kokon bararta, na neman taimakon dalar Amurka miliyan 33 daga kasashen duniya, domin aiwatar da shirin taimakawa kimanin 'yan gudun hijira 150,000 dake kasar Chadi. Har wa yau, MDD na shawarta batun tura tawagar wanzar da zaman lafiya kasar Afirka ta Tsakiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China