in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadan da ke faruwa a Sudan ta Kudu ya shafi yawan man da take hakowa
2014-03-03 10:21:43 cri

Mahukuntan kasar Sudan ta Kudu sun bayyana cewa, sakamakon fadan da ya barke a kasar tun a tsakiyar watan Disamban shekarar da ta gabata tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen da ke goyon bayan korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya haddasa raguwar yawan man da kasar ke hakowa da kusan kashi 30 cikin 100.

Kakakin fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu Ateny Wek Ateny ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai a Khartoum na Sudan, inda ya ce, yawan man da kasar ta saba fitarwa a ko wace rana ya kai ganga 245,000 kafin yakin ya barke, amma yanzu adadin ya ragu zuwa ganga 175,000.

Rahotannin baya-bayan nan na nuna cewa, 'yan tawayen sun rika kai hari kan jihohin Upper Nile da Unity masu arzikin man fetur, kuma har yanzu suna rike da jihohin Bantio, babban birnin jihar Unity, inda ake hako ganga 45,000 a ko wace rana, yayin da ake hako ganga 200,000 a jihar Upper Nile a ko wace rana

A cewar rahotanni MDD, fadan na Sudan ta Kudu ya haddasa mutuwar dubban mutane, kana sama da 67,000 suka tsallaka zuwa kasashe makwabta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China