Cristiano Ronaldo ne ya fara jefa kwallo a ragar Levante, kwallo sa ta 38 a wannan kakar wasanni, wadda ya saka a minti na 11 ta kwanar da Angel di Maria ya dakko.
Duk da cewa Leylor Navas dan asalin kasar Costa Rica ya taka rawar gani, a kokarinsa na tsaron gidan Levante, amma ya kasa tare kwallon da Ronaldo ya mikawa Marcelo, wanda nan take ya sharara ta a ragar a Levanten, mintuna 4 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
A Cikin minti na 63 ne kuma 'yan wasan Levante suka koma mutum 10, bayan da alkalin wasan ya nunawa David Navarro jan kati, bisa tuhumarsa da yiwa Ronaldo keta.
An kai karshen wannan dare mai cike da bacin rai ga kulob din na Levante, bayan da Nikos Karabelas ya ci gidan su, kwallon da ta zama ta 3, mintuna 9 kafin tashi daga wasan. Aka kuma tashi 3 da nema.
Wannan nasara ta sa Real Madrid, zama kan gaba a jerin kulaflikan dake buga gasar ta La Liga, inda kuma ta dara Atletico Madrid dake matsayi na 2 da maki 3, yayin da Bacelona ke matsayi na 3.(Bello Wang)