140306-an-yiwa-kanu-nwanko-aiki-a-zuciya-bello
|
Rahotanni daga cibiyar tallafawa masu ciwon zuciya ta Kanu Nwanko, sun bayyana cewa an yiwa tsohon dan wasan kwallon kafar Super Eagles, kuma mutumin da ya kafa wannan cibiya Kanu Nwanko aiki a zuciyarsa, a wani asibiti dake Cleveland na jihar Ohion kasar Amurka.
A cewar babban jami'i mai lura da cibiyar ta Kanu Nwanko Heart Foundation Mr. Onyebuchi Abia, an yiwa Kanu, da a yanzu haka keda shekaru 37 da haihuwa aikin ne, a karshen makon da ya gabata. Yayin da tsohon dan wasan wanda ya taba bugawa kulaf din Arsenal na kasar Birtani kwallo, ya ziyarci asibiti domin duba lafiyar sa, wanda da ma ya kan yi hakan a kowace shekara.
Kanu dai ya fuskanci matsalar ciyon zuciya a karon farko ne, cikin shekarun 1990, matakin da ya sanya shi kafa cibiyar baiwa yara, da masu rangwamen gata tallafi karkashin cibiyar da ya kafa, wadda kuma har yanzu ke aikin ta a birnin Akijan jihar Legas a tarayyar Najeriya. (Saminu Alhassan)