Ana dai sa ran gudanar wannan gasa ne a kasar Canada daga ranar 5 zuwa 24 ga watan na Agusta dake tafe, wanda kuma kasashe 16 zasu buga wasanni 32 kafin kammalar gasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kasar Sin na rukuni na Biyu ne, tare da Brazil, da Amurka da kuma Jamus. Baya ga Brazil, 'yan wasan kasar ta Sin za su kuma kara da 'yan wasan Jamus, kasar da ta taba lashe wannan kofi har sau Uku, a ranar 8 ga watan Agusta, sai kuma wasan ta na ranar 12 ga watan na Agusta, da mai rike da kambin gasar, wato kasar Amurka, wadda ta dauki wannan kofi har sau Uku.
Wannan ne dai karo na Biyu a jere, da aka hada Sin da kasashen Amurka da Jamus a rukuni guda, inda a shekarar 2012 ma suka kasance tare a rukuni na Hudu.
Bisa tarihin shigar ta wannan gasa, kasar Sin ta kai ga matsayi na Biyu a shekarun 2004 da 2006. ta na cikin kuma kasashen Asiya Uku dake wakiltar nahiyar, ita da Koriya ta Kudu, da Koriya ta Arewa.
Bisa tsarin gasar, mai masaukin baki wato kasar Canada ce zata bude wasa da Ghana, a ranar 5 ga watan Agusta, a birnin Toronto.(Saminu Alhassan)