Yayin wasan Munich da Schelke, dan wasan Munich David Alaba ne ya fara sanyawa kungiyarsa kwallo a zare cikin minti na 3 da take wasan, sai kwallon Robben a minti na 15, kafin shima Mandzukic ya jefa tashi kwallo ta Uku a minti na 24. Robben shi ne ya sake jefa kwallo ta Hudu a zaren Schelke mintuna 4 bayan kwallon Mandzukic. Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma dan wasan Beyern Munich Rafinha ya ci garin su, sakamakon kuskure da ya yi a kokarin fidda kwanar da aka bugo kusa da ragarsu. Hakan ya sanya wasa ya juya zuwa 4-1. Ana tsaka da buga wasa ne kuma aka baiwa dan wasan Schelke jan kati, matakin da ya sanya shi ficewa daga filin wasa, tare da baiwa Munich bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda Robben ya jefa a zare ba tare da wani bata lokaci ba.
Sakamakon wannan wasa dai ya daga matsayin Munich, wadda makinta ya kai 65, yayin da ita kuma Schalke ke a matsayi na 4 da maki 41.
A yayin wasan Dortmund da Nuremberg kuwa, Dormund din ce ta lashe wasan da ci 3 da nema, matakin da ya bata damar sauke Leverkusen daga matsayi na Biyu a teburin gasar.(Saminu Alhassan)