'Yan wasan Roma irin su Gervinho da Adem Ljajic sun yi iyakacin kokarin karya karfin tsaron Inter Milan, amma ba su samu nasarar hakan ba. Har dai karshen wasan 'yan kwallon bangarorin Biyu sun rika kaiwa juna farmaki, amma karfin tsaron bayan gidan Inter Milan, da kuma raunin mafi yawan hare haren da 'yan wasan Roma suka rika kaiwa, ya sanya aka tashi canjaras babu ci.
Kulaf din Inter Milan dai ya dauki kofin wannan gasa ta Serie A har sau 18, yayin da Roma kuma ta dauki wannan kofi sau 3, kuma dukkanin kulaflikan Biyu na sahun gaba, cikin jerin manyan kulaflikan dake taka rawar gani, a fagen wasannin kwallon kafar kasar Italiya.(Saminu Alhassan)