Yayin da yake tabbatar da hakan ga manema labaru, jami'in ma'aikatar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade, ya ce cikin 'yan bindigar da aka cafke a wannan karo, hadda wasu da suka samu damar tserewa farmakin sojojin a baya a wasu sassan birnin Maiduguri da kewaye.
Wannan dai mataki na zuwa ne 'yan kwanaki, bayan da maharan kungiyar ta Boko Haram suka kaddamar da wani hari kan wata makarantar kwana dake jihar Yobe, harin da ya sabbaba rasuwar dalibai da dama, tare da barnata sassan gine-ginen makarantar.
Tuni dai kasar Amurka ta sanya Boko Haram cikin jerin kungiyoyin ta'adda. Har kuma 'yan kwanakin nan, 'ya'yan kungiyar na ci gaba da kaddamar da hare-hare a sassan jahohin nan uku dake arewa maso gabashin kasar. Hare-haren da aka kiyasta cikin watanni ukun da suka gabata kadai, sun hallaka fararen hula sama da 400.
Mahukuntan Najeriyar dai sun kafa dokar ta baci tun cikin shekarar da ta gabata a jihohin na Adamamawa, da Yobe da kuma Borno, a wani mataki na kokarin gaggauta kawo karshen matsalar tsaro da wannan kungiya ke haifarwa. (Saminu Alhassan)