in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a samar da wata kyakkyawar makoma ta bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin
2014-03-06 16:41:40 cri

An shirya taron manema labaru karo na farko na taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a ran 5 ga wata, inda daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Mista Xu Shaoshi, ya zanta da manema labaru kan bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da kuma matakan da gwamnati ta dauka kan manyan fannonin. Mista Xu ya ce, a bana an samu wani mafari mai kyau ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin, kuma za a samar da wata kyakkyawar makoma ta bunkasuwar. Sin tana da sharadi, da kwarewa, da kuma imani wajen cimm burin samun saurin karuwar tattalin arziki zuwa kashi 7.5 bisa dari.

Tun daga shekarar bara har ya zuwa yanzu, an samu bunkasuwar tattalin arzikin yadda ya kamata, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP, ya karu da kashi 7.7 bisa dari a shekarar 2013, yayin da kuma yawan karuwar farashin kayayyakin da jama'a suke saya wato CPI ya kai kashi 2.6 bisa dari.

Yawan sababbin guraban ayyukan yi da aka samar ya kai miliyan 13 da dubu 100, sai kuma yawan karuwar kudin shiga da mazaunan kasar suka samu ya kai kashi 8.1 bisa dari, inda yawan karuwar tattalin arzikin Sin ya kai kashi 30 bisa dari, idan an kwatanta da adadin karuwar tattalin arzikin da aka samu a duk duniya.

Mista Xu Shaoshi ya bayyana cewa, wannan dai sakamako mai kyau, wanda ya wuce abin da aka tsammata a da, a cikinsa akwai abubuwa biyu da suka faru a karon farko.

'Wani abu da ya faru a karon farko shi ne, yawan kayayyaki na shige da fice da Sin ta samu, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 25800, sakamakon hakan ne ma, a karon farko Sin ta zama babbar kasa ta farko a fannin cinikayyar kayayyaki. Wani abu daban da ya faru karo na farko shi ne, yawan darajar sha'anin hidima ya kai kashi 46.1 bisa dari a duk adadin GDP, wanda a karon farko ya wuce sashen da yawan darajar masana'antu ke samarwa a ma'aunin GDP. Lallai wannan ya shaida cewa, kasar Sin ta samu wani babban ci gaba a fannin gyare-gyaren tattalin arziki, kuma tsarin tattalin arzikinta ya canza kwarai da gaske."

Game da zargin da wasu ke yi na tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sin, Mista Xu ya musunta maganar tasu. Ya ce, muhimmin tushen da kasar Sin take da shi wajen tafiyar da harkokin tattalin arziki bai canza ba, Sin tana da sharadi da kwarewa da kuma imani wajen cimma burin samun saurin karuwar tattalin arziki na bana.

'Da farko dai, ayyukan da muke gudanarwa na zurfafa gyare-gyare bisa dukkan fannoni, za su kara inganta karfin tattalin arziki da kwarewar kasuwanni. Na biyu, ayyukan da muke gudanarwa na raya masana'antu, hanyoyin sadarwa, birane da garuruwa, aikin gona ta yadda za su dace da zamani, wadanda za su samar da babbar nasara. Na uku, ayyukan da muke gudanarwa na sa kaimi ga yin kere-kere, za su kara ba mu karfin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci. Na hudu, kyakkyawan sakamakon da muka samu daga matakan da muka dauka bisa manyan fannoni, da kuma niyyar da muke da ita, za su kago wani sharadi mai kyau ga bunkasuwar tattalin arziki.'

Bisa labarin da muka samu, an ce, yawan kudin da za a zuba jari a cikin kasafin gwamnatin tsakiya ya karu, da kudin Sin Yuan biliyan 20, adadin da zai kai ga Yuan biliyan 457.6. Game da haka, Mista Xu ya bayyana cewa,

'Wannan kudi dai, a ganina za a yi amfani da shi wajen daidaita tsarin tattalin arziki, da inganta wasu sassa marasa karfi, ya kamata a yi amfani da kudin a fannonin da ke bukatar canzawa matuka, domin bayar da taimako na gaskiya. Haka muka za a yi amfani da kudin wajen gyare-gyaren wuraren kwana marasa kyau, da gina dakuna domin inganta zaman rayuwar matalauta, da sauran ayyukan more rayuwar al'umma. Kazalika, za a yi amfani da kudin wajen inganta al'amuran da suka shafi kauyuka, da raya aikin gona da kuma manoma, tare da bunkasa fannonin jin dadin jama'a, da gudanar da manyan ayyukan more rayuwar al'umma, da tsimin makamashi, da kare muhalli, da raya yankunan da ke da nisan zuwa, da na kananan kabilu, da habaka kere-kere bisa karfin kwarewar kasar Sin, da kuma daidaita tsare-tsaren ci gaba daban daban.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China