Kwamitin sulhun MDDr ya bayyana hakan ne a daren jiya Jumma'a, tare da bukatar tsagin gwamnati da na 'yan tawayen SPLM-N, da su tabbatar da tsagaita bude wuta. Matakin da kwamitin ke ganin zai taimaka wajen kawo karshen tashe-tashen hankula da ake fuskanta, musamman a jihohin Blue Nile da Kudancin Kordofan na kasar ta Sudan.
A ranar Alhamis 13 ga watan nan ne dai bangarorin Biyu suka koma teburin shawarwari, karkashin kulawar wani babban kwamitin zartaswar kungiyar AU.
Wannan ne kuma karo na Biyu da ake ci gaba da gudanar da tattaunawa, tun bayan jingine shawarwarin a watan Afrilun bara, wanda aka soma a shekarar 2011, inda a wancan lokaci aka tashi ba tare da cimma wata nasara ba.(Saminu Alhassan Usman)