Roy Hodgson ya zabi dan wasan tsakiyar kulaf din Manchester Tom Cleverley ne bisa radin kan sa, matakin da ya janyo nuna rashin amincewar masu goyon bayan kungiyar ta Manchester, da ma da yawa daga masu marawa England baya.
Shafin yanar gizo na Internet mai suna Change.org ya kasancewa wani dandali, da aka kafa tun a shekarar 2007, domin baiwa jama'a masu sha'awar kwallon kafa damar bayyana ra'ayoyin su. Yayin kuma wata kuri'a da aka yi mai taken "Hana Tom Cleverley ya shiga gasa", a kan wannan shafi, sakamako ya nuna cewa, mutane kimanin 7000 ne suka amince da wannan shawara.
Wanda ya gabatar da shawarar ya rubuta a kan shafin cewa, sau 13 Tom Cleverley, ya samu damar shiga gasannin wakiltar kungiyar ta England, adadin da ya haura na Barkley, da Adam Lallana da Osman idan an hada su duka. Sai dai dan wasan ba shi da karfi sosai, don haka masu adawa da sanya shi cikin jerin 'yan wasan ke gani bai cancanta ya wakilci England ba. Wancan mutum na ganin ya kamata a hana Cleverley wannan dama, domin kare martabar kasar a fannin wasan kwallon kafa. Ko da yake dai, tuni aka yi hasashen cewa, da wuya England ta taka wata rawar gani, yayin gasar dake tafe, duk dai da hakan masu wancan ra'ayi na ganin hana shi shiga gasar zai rage yawan asarar da ka iya fadawa kungiyar, ya kuma baiwa sauran 'yan wasan kasar damar bayyana ta su kwarewa.
Tom Cleverley ya buga gasannin Premier League sau 19, a matsayin dan wasan tsakiya, kimar sa da aka fitar a wani shafin yanar gizo mai suna "Who Scored" ta nuna cewa, yana samun matsakaicin maki a cikin dukkanin gasanni da maki 6.81, wanda hakan bai wuce matsayi na 17 kacal, cikin dukkan 'yan wasan Manchester, da suka buga gasanni a wannan karo ba. (Amina)