Babban sakataren FIFA Jerome Valcke ne ya sanar da hakan a ran 1 ga watan nan na Maris, Valcke ya ce 'yan wasan kwallon kafa mata musulmi, suna iya daura dankwali, yayin da kuma maza keda ikon sanya hula da ta dace da launin rigar kungiyar su.
Kafin shekarar 2012 dai, an hana saka duk wani abu daka iya rufe kan dan wasa, saboda kaucewa rauni, ko wani tsautsayi da hakan ka iya janyowa. Sai dai koken da kungiyar kwallon kafa ta nahiyar Asiya AFC ta kai, ya sanya hukumar ta FIFA sake shawarar gwada wannan tsari, na baiwa 'yan wasa damar rufe kokon-kan su, tsawon shekaru biyu domin ganin da cewa, ko akasin hakan. (Amina)