Ban da haka, jaridar Aspen ta fitar da cikakkun jimloli dake kunshe cikin kwangilar da Morata da kulob din na Arsenal suka amincewa, wato bangarorin biyu za su rattaba hannu kan wata kwangila ta tsawon shekaru biyar, inda albashin Morata na kowane mako zai kasance Pound dubu 100.
A nasu bangare kuma, jaridun Globe, da Daily Mail sun bayyana cewa, har zuwa yanzu kulob din kwallon kafar Real Madrid bai bayyana amincewa da hakan a hukunce ba, kasancewar manyan jami'an kulob din na fatan za a bada hayar Moratan na dan lokaci, a madadin sayar da shi.
Duk dai da wannan yanayi da ake ciki kulob din na Real Madrid, ba zai hana Morata tafiya Arsenal ba. Jaridar Transfer Market ta furta cewa, yawan kudin da kulob din Real Madrid ya bukata ya kai Pound miliyan 15, tare da bukatar kulob din na Arsenal, da ya kara wata aya cikin yarjejeniyar cewa, Real Madrid na da ikon sake sayo Alvaro Morata daga Arsenal din a nan gaba.
Dadin dadawa, a kwanan baya, shahararren masani kan sauya shekar 'yan wasa na kasar Spain, Ballagher ya bayyana a shafin jaridar Times cewa, Alvaro Morata ya riga ya amince da sauya sheka zuwa Arsenal, sai dai ana jiran cimma matsaya guda, tsakanin kuloflikan biyu.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu abin da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne, ko kulob din Arsenal zai amince da batun bada hayar Morata zuwa Real Madrid, ko Morata zai sauya sheka zuwa kulob din na Arsenal kai tsaye, ko kuma kulob din Real Madrid zai dakatar da wannan batu a karshe.
A sakamakon jin rauni da takara mai tsanani da 'yan wasa suke yi cikin kulob din Real Madrid, Alvaro Morata ya buga gasar wasani na tsawon mintuna 233 kacal ne, a dukkanin wa'adin gasar kakar wasanni ta bana. Ko da yake kulob na Real Madrid da Carlo Ancelotti, na fatan Morata zai ci gaba da wasan kwallon kafa a kulob din, a zahiri karancin lokacin buga wasanni ya hana bunkasuwar kwarewar Morata, kuma wannan ya kasance muhimmin dalilin da ya sa Real Madrid ba zai dasa shinge ga wannan batu ba.
Bisa darasin da ya samu a da a fannin sauya sheka, kulob din Arsenal ba zai dogara da Morata kawai ba. Bisa labarin da jaridar Daily Sports ta Spain ta bayar, an ce, ana neman sayo Antoine Griezmann dan shekaru 22 a duniya, zuwa kulob din na Arsenal, dan wasan da tauraron sa ke haskawa a 'yan kwanakin baya bayan nan.
An labarta cewa, kudin sauya shekar Griezmann ya kai Pound miliyan 25, ban da kulob na Arsenal, su ma Real Madrid, da Manchester,da Juventus da sauransu na da sha'awa sosai kan Antoine Griezmann.(Fatimah)