in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fletcher na Manchester United na fatan sake farfadowa bayan doguwar jiyya
2014-02-19 21:02:59 cri

Dan wasan tsakiyar kulaf din Manchester United Darren Fletcher, ya bayyana aniyar sa, ta rama shekaru Biyu da ya yi yana jiyya, a sauran lokacin da ya rage masa yana buga kwallo.

Fletcher, dan shekaru 30 ya bayyanawa mujallar Inside United ta kulaf din na Manchester cewa, fatan sa shi ne, ya zarta matsayin da ya bari a baya. Ya ce a ganin sa muddin dan wasa ya gamsu da halin da yake ciki, to kuwa ko shakka babu, ba zai iya wani yunkuri na kara samun nasara ba. Don haka Fletcher wanda dan asalin kasar Scotland ne ke ganin lokaci ya yi, da zai zage damtse, wajen ganin ya maye shekaru Biyun da ya yi yana jiyya da kwazo, irin wanda zai sanya shi zarta sa'a a wannan kungiya ta Manchester United da yake bugawa kwallo.

Fletcher dai ya sha fama da wani ciwo a hanjin sa, wanda ya hana shi damar ci gaba da wasa tun makon karshe na shekarar 2012. Ya kuma buga wasan sa na farko bayan dawowar sa daga jiyya ne, a wasan gasar Premier da ya gabata, cikin watan Disambar bara, wasan da Manchester ta lallasa Aston Villa da ci 3 da nema.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China