in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manajan Kulaf din kasar Ingila ya yaba da farfadowar Raheem Sterling
2014-02-19 21:01:49 cri
Babban mai horas da 'yan wasan Kulaf din kasar Ingila Roy Hodgson, ya yaba da farfadowar da dan wasan kasar sa, kuma dan gaban kungiyar Liverpool Raheem Sterling ke yi a yanzu haka.

Hodgson ya ce Sterling mai shekaru 19 da haihuwa, na kara bayyana kwarewarsa a fagen taka leda yanzu haka a Liverpool, bayan koma baya da ya samu. Yace yadda dan wasan ke taka ya nuna alamun cewa, zai taka rawar gani a gasar cin kofin duniya dake tafe a Brazil. Kocin Ingilan ya kara da cewa, ba zai manta da irin rawar da wannan dan wasa ya taka, yayin gasar cin kofin 'yan kasa da shekaru 21, da kasar sa ta buga da Scotland a bazarar shekarar da ta gabata ba, inda dan wasan ya taka kyakkyawar rawar da ta dace.

Hodgson ya yi fatan abinda ake gani yanzu haka daga matashin dan wasan, zai dore yayin wasannin gasar cin kofin duniya da Ingilan za ta buga a Brazil.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China