in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaflikan kwallon kafar Angola sun samu nasarar kara matsawa gaba a gasar cin kofin hukumar CAF
2014-02-19 21:00:38 cri
Kulaflikan Petro Atletico, da Desportivo Huila na kasar Angola, sun samu nasarar lashe wasannin share fage da suka buga, da kwallaye uku-uku a ragar abokanan karawarsu, a ci gaba da ake yi da share fagen gasar cin kofin hukumar gudanarwar kwallon kafar Afirka ta CAF. Nasarar da kuma ta basu damar shiga zagayen farko na gasar.

Shi dai kulaf din Petro Atletico, ya samu nasarar jefa kwallaye 3 a zaren kulaf din African Stars na kasar Namibia, a wasan da suka buga a karshen mako a gidan kulaf din Petro, wanda hakan ya ba shi damar goge kwallaye 2 da African Stars din ta jefa masa a gidan ta yayin wasan su na farko.

Kulaf din African Stars wanda ya ke tsammanin samun karin nasara, bayan tashin sa wasan farko a gida da ci 2 da nema, ya sha mamaki, bayan da dan wasan sa Hartman Toromba ya ci gidansu mintuna 2 da take wasa, sai kuma kwallon Ladji Keita ta biyo baya mintuna 2 kafin tafiya hutun rabin lokaci. Kafin Ladji ya kara kwallo ta Uku.

Shima kulaf din Desportivo Huila ya samu nasarar wasan da ya buga da CF Mounana na kasar Gabon, a filin wasa na Estadio Tundavala dake Kudancin birnin Lubango, da ci uku da babu.

Dan wasan Huila Aly shi ne ya fara zurawa kulaf din sa kwallon farko, mintuna 7 kafin tafiya hutun rabin lokaci, sai kuma kwallon da Lito ya sanya a raga a tsakiyar zagaye na Biyu na wasan. A kuma kimanin mintuna 10 da tashi wasan ne, Pataca ya sanya kwallo ta Uku ga kungiyar ta Huil. A yanzu haka dai kulaf din CA Bizertin, wanda ya sha kashi a hannun zakaran gasar kulaflikan kasar Tunisiya CS Sfaxien a wasan kusa da na karshe a bara, shi ne zai kara da kulaf din Desportivo a zagayen farko na gasar CAF.

Har wa yau shima kulaf din kasar Mozambic Ferroviario Beira ya samu nasarar lashe takwaransa na Tanzaniya wato Azam da ci 2 da nema. Sakamakon kwallaye 2 da dan wasan gaban sa Mario Simamunda ya zura.

Yanzu haka dai a wasan zagayen farkon da za a shiga, kulaf din na Ferroviario zai kece raini ne da Zesco United na kasar Zambiya, wanda shi ma ke cikin kulaflika 11 da suka tsallaka zuwa zagayen gasar na farko.

Sauran kulaflikan da ake sa ran za su nuna bajinta a zagayen gasar CAF din na farko dai sun hada da AFC Leopards na kasar Kenya, wanda zai kara a wasan farko da Super Sport United na kasar Afirka ta Kudu. Akwai kuma kulaf din Saint Michel United na tsibirin Seychelles wanda zai kara da kulaf din How Mine na Zimbabwe.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China