Xavi ya bayyana hakan ne don nuna goyon bayan sa ga Messi, wanda wasu masu nazartar al'amuran kwallon kafa ke ganin ya gaza, wajen jagorantar kungiyar kasar sa ta Argentina, kaiwa ga wuce zagayen kusa da na karshe, a gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Jamus a shekarar 2006, da kuma Afirka ta Kudu a shekarar 2010. Har wa yau an bayyana rashin gamsuwa kan yadda Messi yake taka leda a kungiyar kasar ta sa ta Argentina.
Sai dai a hannu guda Xavi a nasa bangaren ya kare abokin wasan na sa, ya na mai cewa, Messi ya riga ya tabbatar da matsayinsa na zakarin gwajin dafi, ganin yadda yake taka muhimmiyar rawa a ko wane wasan da ya buga cikin shekaru 6 ko 7 da suka gabata.
An ce Messi dan shekaru 26 da haihuwa, ya kasance cikin yanayi mai kyau a makonni baya bayan nan, bayan da ya dan gamu da matsala wajen kokarin biyan bukatun jama'a, lokacin da ya dawo filin wasa daga jinyar da ya yi ta wani rauni.
A kakar wasanni ta La Liga a wannan karo, Messi ya riga ya buga wasanni 17, ya kuma ci kwallaye 13. A wasanni 3 da suka gabata kawai, ya ciwa kungiyar sa ta Barcelona kwallaye 5.(Bello Wang)