Kafin take wannan wasa dai sai da Yaya Toure dan asalin kasar kwadibua, ya bayyana cewa shafe shekaru 3 yana takawa kulaf din Barca kwallo da yayi a baya, ya bashi damar samun fasahohi masu inganci, ya kuma yi abokai da dama kafin komawarsa Manchester City. Yace fuskantar wadannan abokan wasansa a matsayin abokin hamayya ba abu ne mai sauki ba.
Toure ya bayyanawa wakilin shafin yanar gizo na UEFA.com cewa, ba ya so ya kara da Barca a gaban jama'ar da a baya, suka rika nuna masa goyon baya da kauna, sai dai a cewarsa hakan ya zama dole tunda haka kwallo ta gada.
Don gane da banbancin rawar da yake takawa a kulaflikan Biyu, Toure ya ce komawar sa Man City ya bashi damar sauya wuraren taka leda tun daga tsakiya, gefe da kuma bayan kungiyar, sabanin zaman sa a Barca, inda ya ke buga tsakiya kadai. Bugu da kari Toure ya ce ya fi son salon kwallon kulaflikan kasar Ingila, wanda ke tattare da kai hare-hare cikin saurin gaske.(Bello Wang)