Maharan sun kaddamar da harin ne da safiyar ranar Alhamis a garin Michika kimanin kilomita 280 daga Yola, babban birnin jihar ta Adamawa, inda suka rika jefa abubuwa fashewa kan wasu bankuna, shaguna da wuraren kasuwanci da ke garin.
Bugu da kari, rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa, maharan sun kuma kai hari kan ofishin 'yan sanda da ke garin Michika, inda suka halaka wasu daga cikin jami'anta.
Shugaban karamar hukumar Michika, Ulama Maina ya tabbatar wa manema labarai abkuwar lamarin, yana mai cewa, harin ya cusa jama'a cikin rudani har ma wasu mazauna wurin sun gudu zuwa barikokin soja da na 'yan sanda, amma bai yi wani karin bayani ba.
Shi ma jami'in hulda da jama'a na birget din soja ta 23 dake Yalo, Kyaftin Nuhu Jafaru, ya tabbatar da abkuwar harin, amma shi bai yi karin haske ba. (Ibrahim)