Alade ta bayar da wannan tabbacin ne ranar Jumma'a, yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, inda ta tabbatar wa masu ruwa da tsaki a harkar banki, ciki har da al'ummomin kasa da kasa cewa, canjin da aka samu a babban bankin kasar ta Najeriya, ba zai taba shafar manufofin kudin kasar ba, ganin cewa, alkaluman hukumar kididdigar kasar sun nuna cewa, adadin hauhawan farashin kaya a kasar kashi 8 cikin 100 ne kawai.
Don haka ta bayar da tabbacin cewa, bankin karkashin jagorancinta zai himmantu wajen tabbatar da nasarorin da ya riga ya cimma, ta hanyar martaba manufofin kudi don tabbatar da daidaiton farashin kaya da manufofin kudi.
Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis ne shugaba Goodluck Jonathan ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar Malam Sanusi Lamido Sanusi, kana ya umarci mataimakiyarsa Madam Sarah Alade da ta karbi ragamar harkokin bankin. (Ibrahim)