Rahotanni da kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua ya tattara, sun bayyana cewa, tuni jami'an karamar hukumar ta Bama suka mika gawawwakin mutanen ga iyalansu domin binne su.
Shi kuwa shugaban kungiyar 'yan aikin tsaro na sa kai dake yankin Akura Satomi, cewa ya yi mutane 96 ne kungiyarsa ta tantance, biyowa bayan harin da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da shi.
Baya ga wadanda suka rasa rayukansu, harin na garin Bama ya sabbaba jikkatar mutane da dama, tare da asarar dukiya mai tarin yawa, sakamakon kone gidaje, kantuna da tashar motar garin da maharani suka yi. Maharan sun kuma kai farmaki fadar hakimin Baman Kyari Ibn Ibrahim, koda yake dai ya tsira da ransa.
Tuni dai gwamnan jihar ta Borno Kashim Shettima, ya jaddada kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta fiddo da sabbin matakan dakile ayyukan kungiyar ta Boko Haram, wadda yanzu haka ke dada tsananta kai hare hare a sassan jihar daban daban. (Saminu Alhassan)